Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sayyid AbdulMalik Badruddin ya ce Isra'ila ta jefa tsaron yankin baki daya da ma duniya baki daya cikin hadari.
Domin Amurka akan dole ta shiga wani tsagaita bude wuta da Iran. Tsagaita wuta da ake yi a yanzu ya faru ne saboda tilastawa Amurka da Isra'ila bayan gagarumin rashin nasarar da suka yi wajen cimma burinsu. A sahun gaba na manufofin kai hari Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne hambarar da tsarin Musulunci da mamaye al'ummar musulmi ta Iran amma hakan yaci tura. Shugaban Yamen ya kara da cewa: kai harin Amurka a Isfahan ya gaza gaba daya. Amurka ta yi asarar jiragen sama da dama, da suka hada da jiragen dakon man fetur da AWACS wanda ya haifar da shan kayen Amurka a Isfahan. Yakin ya kawo tsadar tattalin arziki ga Washington da Tel Aviv, kuma ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da tabarbarewar harkar kudi a kasuwannin duniya.
Amurka da Isra'ila ba su da wata hujja ta kai hari Iran da haifar da barazanar zaman lafiya a yankin da duniya.
Jagoran Ansarullah Yemen: A cikin yakin da aka yi kwanan nan, Fagen gwagwarmaya ya dunƙule ya haɗu a ɗakin bayar da umarni ɗaya; Wannan babbar nasara ce.
Your Comment